An kori mai kulob din Leads United

Hakkin mallakar hoto empics
Image caption Wata kotun Italiya ce ta samu Cellino da laifin kauce wa biyan haraji

Hukumar gudanar da gasar League ta turai ta kori mamallakin kulob din Leads United Massimo Cellino, ta kuma umarce shi da ya yi ritaya.

Hukumar ta yanke wannan hukuncin ne bayan da ta samu takardu daga wata kotun Italiya wadda ta samu Cellino da laifin kaucewa biyan haraji.

Cellino mai shekaru 58, zai iya komawa kan kujerarsa ranar 18 ga watan Maris a badi, kuma zai iya daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa.

A watan Maris, an ci tarar Cellino fam dubu 502 bayan da aka same shi da laifin kin biyan kudin fiton jirgin ruwan shakatawasa.