An tsawaita kwantaragin Gerrard

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Rodgers ya musanta cewa ba ya jituwa da Gerrard

Kociyan Liverpool, Brendan Rodgers ya ce an tsawaita kwantaragin dan wasan kungiyar, Steven Gerrard.

Ya karyata rade-radin da ake yi cewa ba sa shiri da dan wasan.

A lokacin da manema labarai suke yi masa tambayoyi dangane da rashin jituwarsa da Gerrard, a wani taron manema labarai gabanin wasan Premier at Leicester ranar Talata, Rodgers ya ce ko alama hakan ba gaskiya ba ne.

Rodgers ya kara da cewa za a bai wa Gerrard dama domin ya yi wa kwantaragin duban tsanaki, sai dai kuma ya ce batun kudi ba zai zama matsala ba.

Hakan ba kawai zai yi tasiri a rayuwarsa ba ne kadai, zai ma taimaka masa wajen tantance inda zai yi kwantaraginsa, in ji Rodgers.