Klopp ya ce ba zai ajiye kocin Dortmund ba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Klopp ya dauki alhakin rashin taka rawar ganin klob din a gasar Bundesliga

Kocin Borussia Dortmund Jurgen Klopp ya ce ba zai ajiye aikinsa ba, duk da cewa ya dauki alhakin rashin taka rawar gani da klob din ya yi a gasar Bundesliga.

Dortmund wadda ta zo ta biyu a gasar bara, yanzu tana kasan tebur bayan ta buga wasanni 13, inda ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Eintracht Frankfurt ranar Asabar.

Klopp wanda ya kai Dortmund wasan kusa da na karshe a gasar zakarun turai a 2013, ya ce ba zai yi ritaya ba.

Klob din Dortmund wanda ke da maki 11 a teburin gasar Bundesliga bayan wasanni 13, ya koma kasan tebur bayan da Werder Bremen da Stuttgart suka samu nasara.