Liverpool za ta tsawaita kwantiragin Gerrard

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A watan Nuwamban 1998 Gerrard ya fara buga wa Liverpool wasa

Klob din Liverpool ya yi wa Steven Gerrard tayin tsawaita kwantiraginsa in ji Koci Brendan Rodgers.

Haka kuma Rodgers ya karyata cewa sun samu sabani da Gerrard wanda kwantiraginsa za ta kare da klob din a karshen kakar wasannin bana.

Kocin ya ce za a bai wa Gerrard lokaci ya yi tunani a kan tayin da aka yi masa, amma kudin kwantiraginsa ba zai kawo tsaiko ba.

Gerrad ya fara bugawa Liverpool wasa ne a ranar 29 ga watan Nuwamba 1998, a karawar da suka yi da Blackburn Rovers, kuma ya buga wasanni 687 ya kuma zura kwallaye 176 a raga.