Man City ta kama hanyar cin Premier-Pellegrini

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Pellegrini ya ce 'yan wasan Man City suna da hazaka ta neman nasara koda yaushe

Mai horas da 'yan wasan Manchester City, Manuel Pellegrini ya ce nasarar da klob din ya samu a karawar su da Southampton ta nuna cewa zasu iya haramta wa Chelsea kofin Premier.

City ta zama ta biyu a teburin Premier bayan ta lallasa Southampton da ci 3-0, kuma maki 6 ne ya raba su da Chelsea da ke saman teburin.

Pellegrini ya ce "za mu iya yin korafin abubuwa da yawa a cikin klob din, amma abu guda da ba za mu yi korafi a kai ba, shi ne 'yan wasanmu suna da hazaka da kwar jini da kuma burin ci gaba da samun nasara''.

Kocin ya ce yana da kwarin gwiwar a kwai isasshen lokaci da za su kamo Chelsea, wadda ta buga kunnen doki 0-0 da Sunderland ranar Asabar.