Valencia za ta kori wani mai goyon bayanta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi bai samu rauni ba lokacin da aka jefe shi

Kungiyar Valencia ta ce za ta kori wani mai goyon bayanta har abada saboda ya jefi dan wasan Barcelona, Lionel Messi a kai da robar lemu a wasan Laliga da suka buga ranar Lahadi.

An jefi Messi dan shekaru 27 lokacin da 'yan wasan Barcelona ke murnar zura kwallon da Sergio Busquets ya yi.

Messi bai samu rauni ba, amma Valencia cikin wata sanarwa ta ce ta yi bakin ciki da al'amarin.

A ranar da aka jefi Messi, wani dan kallo ya mutu bayan rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan Atletico Madrid da Deportivo La Coruna.