Za a raba rukunin gasar cin kofin Afirka

Afcon Draw Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashe 16 ne za a raba su zuwa rukuni 4 da zai kunshi kasashe hudu

Zambia da Equatorial Guinea suna cikin kasashen da suke sahun farko, a lokacin da za a raba jaddawalin fara gasar cin kofin nahiyar Afirka na badi.

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF za ta raba kasashe 16 ne rukunnai hudu, domin fitar da yadda za su kara a gasar da za a fara daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun badi.

CAF za ta raba kasashen ne bisa kokarin da suka yi a gasar karo uku baya da kuma yadda suka fafata wajen neman tikin shiga wasannin a tsawon gasa uku baya.

Haka kuma hukumar ta yi la'akari da yadda kasashen suka kokarta wajen samun tikitin shiga gasar badi da aka kammala.

Za a raba jaddawalin fara gasar kofin nahiyar Afirka ne ranar Laraba, wanda za a gudanar a Malabo, Equitorial Guinea.