Kolo Toure zai yi ritaya bayan kofin Afirka

Kolo Toure Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya buga wa Ivory Coast wasanni 109

Dan kwallon Ivory Coast Kolo Toure, ya ce zai yi ritayar buga wa kasarsa tamaula bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka na badi.

Dan wasan mai shekaru 33, wanda ke buga wasa a Liverpool ya fara buga wa Ivory Coast wasa ne a karawar da ta yi da Rwanda a shekarar 2000, kuma ya buga wasanni 109.

Toure yana cikin 'yan wasan da suka samawa Ivory Coast tikitin zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka, kuma ana sa ran zai buga mata wasannin da za a fara a Janairun badi.

Dan wasan yana cikin wadan da suka buga gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil, sai dai wasa daya kacal ya buga wa Ivory Coast, wanda ta kara da Girka.