Pele yana samun sauki a asibiti

Pele Brazil Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun a ranar 13 ga watan Numamba ne aka fara kai Pele asibiti

Pele yana samun sauki, ya kuma bar sashin kulawar gaggawa, bayan da aka yi masa aiki kan cutar mafitsara.

An kai Pele tsohon dan kwallon Brazi, wanda ya lashe kofin duniya sau uku aibitin Albert Einstein da ke Sao Paulo ranar Asabar 24 ga watan Nuwamba.

Tun a ranar 13 ga watan Nuwambar ne aka yi wa Pele tiyata, a inda aka cire masa tsakuwa a kodarsa.

Ana yi wa Pele kallon dan kwallon da yafi yin fice a duniya, bayan da ya zura kwallaye 1, 281 a raga a wasanni 1,363 cikin shekaru 21 da ya buga tamaula.