An yi zuben kasashen da za su fafata a kofin Afirka

Afcon Cup Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption za a fara wasannin ne daga 17 ga watan Janairun badi

An saka kasashen da za su fafata a gasar cin kofin nahiyar Afirka cikin rukunai. Gasar da kasar Equitorial Guinea za ta karbi bakunci a badi.

Jadawalin da kasashen da aka yi a Malabo ya kasa kasahe 16, zuwa rukunnai hudu, kowane dauke da kasashe hudu.

Kasar Algeria wadda tafi yin fice a kwallon kafa a Afirka tana rukuni na uku da ya kunshi kasashen Senegal da Ghana da kuma Afirka ta Kudu.

Rukunin farko ya kunshi mai masaukin baki Equitorial Guinea da Gabon da Congo da kuma Burkina Faso.

Za a fara gasar cin kofin kwallon kafar na Afirka mafi girma a ranar 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun badi.

Ga yadda aka raba kasashen a cikin rukunnan gasar kofin Afirkar:

Group A: Equatorial Guinea, Congo, Gabon, Burkina Faso

Group B: Zambia, DR Congo, Cape Verde, Tunisia

Group C: Ghana, Senegal, South Africa, Algeria

Group D: Ivory Coast, Guinea, Cameroon, Mali