An bukaci Beckham ya gaggauta kafa kulob

David Beckham Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Beckham ya kammala wasansa a kulob din PSG

Kwamishinan gasar kwallon kafar Amurka wato MLS, Don Garber, ya gargadi David Beckham da ya kammala bude sabon kulob dinsa na Miami.

Sau biyu hukumar kwallon kafar Amurka tana kin amincewa da tsare tsaren da Beckham, tsohon kyaftin din Ingila, ya gabatar mata kan filin wasa mai daukar 'yan kallo 25,000.

A wannan makon ne hukumar MLS za ta nazarci hanyoyin da za ta bunkasa wasannin kwallon kafa a Amurka, sannan ta aiwatar da shawarwarin da ta yanke a farkon badin.

Beckham, tsohon dan kwallon United, ya fada a bara cewar idan ya yi ritaya zai iya buga wa kulob din tamaula duk da har yanzu bai rada masa suna ba.