Costa ba zai buga karawa da Tottenham ba

Diego Costa Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Costa ya zura kwallaye 11 a gasar Premier bana

Dan kwallon Chelsea Diego Costa ba zai buga karawar da kulob dinsa zai yi da Tottenham ba a gasar Premier wasan mako na 14 ranar Laraba.

Costa, ba zai buga wasan ba ne sakamakon katin gargadi na biyar da aka ba shi a karawar da suka yi da Sunderland ranar Asabar.

Chelsea wadda take matsayi na daya a teburin Premier, za ta karbi bakuncin Tottenham wadda take mataki na tara a teburi a wasan hamayya a Stamford Bridge.

Tottenham na fama da 'yan wasa da suke jinya wadanda ba za su buga wasan ba da suka hada da Emmanuel Adebayor da Etienne Capoue da kuma Danny Rose.