Kwadwo ba zai buga kofin Afirka ba

Kwadwo Asamoah Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya buga wa Ghana wasanni karo 66

Dan Kwallon Ghana, Kwadwo Asamoah, zai yi jinyar watanni uku, kuma ba zai buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a fara a badi ba.

Ranar Talata ne aka yi wa dan wasan, mai shekaru 25, wanda yake buga tamaula a Juventus ta Italiya tiyata.

Asamoah ya kuma yi jinya a watan Nuwamba, dalilin da ya sa bai buga wa Ghana wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Afirka guda biyu ba.

Dan wasan ya buga wa Ghana wasanni 66 ya kuma zura kwallaye hudu a raga.