'Manchester City na daf da morar jarinta'

Khaldoon Al Mubarak Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City tana matsayi na biyu a teburin Premier

Shugaban kulob din Manchester City Khaldoon Al Mubarak ya ce suna daf da fara cin ribar dimbin jarin da aka zuba don kara karfafa shi.

Kulob din, wanda ke buga gasar Premier, na daf da mai da kudin da aka zuba masa, duk da cewar ya sanar da faduwar sama da fam miliyan 22 a karshen watan Mayun 2014.

Faduwar da kulob din ya sanar ta hada da sama da fam miliyan 16 da hukumar kwallon kafar Turai ya ci tararsa, sakamakon karya ka'idar daidaita kashe kudin kulob.

Mamallakin Manchester City Sheikh Mansour ya zuba kudi da ya kai fam biliyan daya tun lokacin da ya sayi kulob din a shekarar 2008.