Likitoci za su dauki hoton gwiwar Rooney

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto AP
Image caption United tana matsayi na hudu a teburin Premier

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce likitoci za su dauki hoton gwiwar Wayne Rooney, domin auna raunin da ya ji.

Rooney, mai sheakaru 29, ya ji rauni ne a karawar da United ta doke Hull City, kuma ya buga karawar da kulob dinsa ya doke Stoke City da ci 2-1 a gasar Premier da suka buga ranar Talata.

United tana fama da sakamakon jin raunin da 'yan wasanta ke yi tun lokacin da Van Gaal ya karbi aiki a hannun David Moyes a kakar wasan bana.

United tana matsayi na hudu a teburin Premier, bayan da ta buga wasanni 14, kuma za ta ziyarci Southampton a ranar Litinin.

Jerin 'yan wasan United da suka yi jinya tun fara kakar wasan bana

Angel Di Maria da Juan Mata da Michael Carrick da Daley Blind da Ashley Young da Ander Herrera da Antonio Valencia da Anderson da Marouane Fellaini da kuma Jesse Lingard

Sauran 'yan wasan sun hada da Rafael da Luke Shaw da Phil Jones da Marcos Rojo da Jonny Evans da Chris Smalling da Paddy McNair da David De Gea da kuma Tom Thorpe.

Suma Radamel Falcao da Wayne Rooney da Robin van Persie da kuma James Wilson sun yi jinya.