Za a fara aikin fadada filin Anfield

Liverpool Anfield
Image caption Za a kammala aikin kafin fara gasar wasanni ta 2016/17

Kulob din Liverpool ya ce zai fara aikin fadada filin wasansa na Anfield, domin ya samu karin 'yan kallo daga 45,500 zuwa 59,000.

Kungiyar ta Liverpool, wadda za ta kashe fam miliyan 100 wajen aikin, ta kammala sayen gine-ginen da ke kusa da filin, da zai ba ta damar fara aiki gadan-gadan.

Ranar Litinin ne za a fara aikin fadada sashen 'yan kallo inda za a kara gina shiyya ta uku; hakan kuma zai samar da karin kujerun 'yan kallo 8,300.

Za kuma a fadada sashen 'yan kallo na titin Anfield inda za a samar da karin kujerun 'yan kallo 4,800.

Ana sa ran za a kammala aikin fadada yawan 'yan kallon kulob din kafin fara gasar wasanni ta 2016-17. Hakan zai taimakawa kulob din karin samun kudin shiga.