Za a bai wa Drogba aikin da ba na buga kwallo ba

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Drogba na dab da yin ritaya

Mai horas da 'yan wasan Chelsea, Jose Mourinho ya ce zai bai wa dan wasan kungiyar Didier Drogba aikin da ba na buga kwallo ba ne idan ya yi ritaya.

Dan wasan, mai shekaru 36, ya zura kwallo a wasan da suka doke Tottenham da ci 3-0 ranar Laraba.

Mourinho ya ce, "abu ma fi muhimmanci shi ne kasancewa yana tare da mu, kuma zai gama taka leda a Chelsea. Sai dai a gani na zai ci gaba da yin wasu ayyukan na daban ko da ya kammala wa'adinsa na buga kwallo a nan."

Drogba ya dauki kofuna 10 a kwantaraginsa na farko da Chelsea tsakanin shekarar 2004 da 2012, sannan ya zura kwallaye 157 a wasanni 341 da ya bugawa kungiyar.

Ya sake komawa kungiyar ne a farkon kakar wasanni bayan ya bar kungiyar Galatasaray ta kasar Turkiyya.