Ghana za ta dawo da Muntari da Boateng

Boateng and Muntari
Image caption Ghana ta dakatar da 'yan wasan ne bayan gasar cin kofin duniya

Sabon kocin tawagar Ghana, Avram Grant, ya ce kofa a bude take ga Sulley Muntari da Kevin-Prince Boateng, su dawo buga wa tawagar kasar kwallon kafa.

'Yan wasan biyu an dakatar da sune sakamakon halin rashin da'a da su ka nuna a lokacin da suka wakilci Ghana a gasar kofin duniya da aka kammala a Brazil.

Sai dai kuma Grant, ya ce kofa a bude take ga dukkan dan kwallon Ghana ya bayar da gudunmawarsa ga kasar, amma akwai sharudda.

An hukunta Muntari bayan da aka same shi da laifin cin mutuncin mamban hukumar kwallon kafar Ghana, yayin da aka sami Boateng da kin yin biyayya ga koci Kwesi Appiah.