Aguero yana kan ganiyarsa — Pellegrini

Sergio Aguero
Image caption Aguero ya zura kwallaye 14 a raga a gasar Premier bana

Kocin Manchester City, Manuel Pellegrini, ya ce Sergio Aguero yana kan ganiyarsa, kuma zai ci gaba da taka rawar gani.

Aguero dan kasar Argentina, mai shekaru 26, ya zura kwallaye 19 a wasannin Premier da gasar cin kofin zakarun Turai da ya buga.

Dan wasan ya zura kwallaye biyu a raga a wasan da suka doke Sunderland da ci 4-1 a gasar Premier a ranar Laraba.

Manchester City za ta karbi bakuncin Everton a filin Ettihad a gasar Premier wasan mako na 15 ranar Asabar.