Southampton za ta dauko 'yan wasa a Janairu

Ronald Koeman Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Southampton ta ya rashin nasara a hannun Arsenal a gasar Premier

Kocin Southampton Ronald Koeman ya ce zai yi kokari ya kara dauko 'yan wasa a watan Janairu, ganin yadda 'yan wasansa uku suka samu rauni.

Southampton ta karasa wasan da Arsenal ta doke ta da ci daya mai ban haushi da 'yan wasa goma a fili, bayan da Toby Alderweireld ya ji rauni kuma lokacin ta gama sauya 'yan wasanta uku.

Koeman ya ce 'yan wasan da suke buga wasan tsakiya sun fi jin rauni a kai a kai, abin da yasa suke shiga cikin matsala kenan.

Southampton za ta karbi bakuncin Manchester United a gasar cin kofin Premier a wasan mako na 15 ranar Litinin.