Canada 2015: Nigeria tana rukuni daya da Amurka

Asisat Oshoala Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashe uku ne za su wakilci Afirka da suka hada da Nigeria da Ivory Coast da kuma Kamaru

An raba jaddawalin fara gasar cin kofin duniya ta mata da Canada za ta karbi bakunci a badi, yayin da aka saka Nigeria a cikin rukuni mai zafi.

Super Falcons wadda ta lashe kofin Afirka an hada ta rukuni na hudu da ya kunshi Amurka da Sweden da kuma Australia da za su fafata a filin wasa na Winnipeg.

Ivory Coast za ta buga wasanninta ne a filin wasa na Ottawa, a cikin rukuni da ya kunshi Jamus da Norway da kuma Thailand a rukuni na biyu.

Kamaru tana rukuni na uku wanda ya kunshi Japan da Switzerland da kuma Ecuador. Inda za su kara da a filin wasa na Vancouver.

Za a fara wasannin cin kofin duniyar ne na kwallon kafar Mata daga 6 ga watan Yuni zuwa 5 ga watan Yulin badi.

Ga yadda aka raba jaddawalin wasannin:

Group A Canada, China, New Zealand, Netherlands

Group B Germany, Ivory Coast, Norway, Thailand

Group C Japan, Switzerland, Cameroon, Ecuador

Group D USA, Australia, Sweden, Nigeria

Group E Brazil, South Korea, Spain, Costa Rica

Group F France, England, Colombia, Mexico