West Ham ta doke Swansea da ci 3-1

West Ham Swansea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Swansea ta dare matsayi na uku a teburi da maki 27

West Ham United ta doke Swansea da ci 3-1 a gasar Premier wasan mako na 15 da suka buga a Upton Park, ta kuma dare matsayi na uku a teburin Premier.

Swansea ce ta fara zura kwallo ta hannun Wilfried Bony, kafin daga baya Andy Carroll ya farke kwallo, wanda rabonsa da ya ci kwallo tun a watan Maris.

Bony ya kusa ya kara kwallo ta biyu a raga lokacin da ya buga kwallo ta bugi turki, inda West Ham ta kara kwallonta na biyu ta hannun Andy Caroll.

A wasan sai korar golan Swansea Lukasz Fabianski aka yi, sakamakon ketar da ya yiwa Diafra Sakho, kafin Sakhon ya kara kwallo ta uku a karawar.

West Ham ta dare matsayi na uku a teburin Premier, ita kuwa Swansea rabonta da lashe wasa tun lokacin da ta doke United a wasan farko na gasar Premier.