Lineker ya yi tur da masu zagin Wenger

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Arsenal tana matsayi na shida a teburin Premier bana

Tsohon dan kwallon Ingila, Gary Lineker, ya soki magoya bayan Arsenal wadan da suka yi wa Arsene Wenger ihu, bayan kammala wasa da Stoke City.

An nuna wani faifan bidiyo da ya nuna wasu magoya bayan Arsenal suna yi wa Wenger ihu lokacin da zai shiga jirgin kasa, bayan kammala wasan da Stoke ta doke su da ci 3-2 ranar Asabar.

Lineker ya ce bai kamata ba, kuma ba abu ne da za a amince da shi ba, domin rashin kyautawa ne.

A bayan nan Wenger ya kuma fuskanci kalubale a wajen magoya bayan kulob din lokacin da West Brom ta doke Arsenal da ci daya mai ban haushi.

Magoya bayan sun daga wani kyalle mai sakon "Mun gode wa Arsene da gudunmawar da ka bayar, amma lokaci ya yi da ya kamata kayi ban kwana".

Arsenal ta kawo kamfar kofi da ta yi na tsawon shekaru tara, bayan da ta lashe kofin FA a watan Mayu, kuma rabonta da kofin Premier tun 2004, yanzu tana matsayi na shida a teburin Premier.