'Minti 20 kacal Falcao zai iya buga wasa'

Radamel Falcao
Image caption Falcao ya ce sai an saka shi a wasa ne zai iya dawo wa kan ganiyarsa

Kocin Manchester United, Louis van Gaal, ya ce Radamel Falcao minti 20 kacal zai iya buga wa kulob din tamaula a wasa.

Van Gaal ya ce ya yanke hakan ne sakamakon dan kwallon Colombia baya kan ganiyarsa, wanda sau biyu United ba ta fara wasa da shi a karo biyu baya da ta buga wasanni.

Kyaftin din United Wayne Rooney yana jinya, wanda ba zai buga wasan da United za ta kara da Stoke City ba, tuni kuma ta maye gurbinsa da James Wilson maimakon ta saka Falcao.

Van Gaal ya ce Falcao ba ya kan ganiyarsa, kuma ya kamata ya dawo da tagomashinsa, domin shi ya kamata ya maye gurbin Rooney, "To amma nasan ba zai iya buga wasa fiye da minti 20 ba".