Man United za ta kara dauko 'yan wasa

Old Trafford Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United ta koma matsayi na uku a teburin Premier

Manchester United ta sanar da cewar za ta sake dauko 'yan wasa, bayan da kulob din ya sanar da sayar da hannayen jarin miliyan daya.

Edward Glazer, wanda ya gaji United a hannun babansa Malcolm wanda ya mutu a bara, shi ne ya sanar da sayar da hannayen jarin kulob din.

Tun a watan Mayun bara ne dai aka rabawa Edward tare da 'yan uwansa shida gadon hannayen jarin Manchester United din.

Bayan da United ta kasa samun tikitin buga gasar cin kofin zakarun Turai a bara, sabon koci Louis van Gaal ya kashe sama da fam miliyan 150 wajen dauko sabbin 'yan wasa.