Wenger zai rufe bakin masu yin korafi a kansa

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Wenger na fatan dawo da tagomashin Arsenal

Kocin Arsenal Arsene Wenger na fatan rufe bakin masu yin korafi a kansa, idan ya doke Galatasaray a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata.

Gunners tana matsayi na shida a teburin Premier, kuma an nuna wani faifan bidiyo da magoya bayan Arsenal suka yi wa Wenger ihu a tashar jirgin kasa.

Wenger ya ce suna cikin matsi, kuma hakan na daya daga cikin kalubalen da masu horar wa suke fuskanta a lokuta da dama.

Arsenal wadda ta samu kai wa wasan zagayen gaba a gasar zakarun Turan, za ta kara da Galatasaray da ke da maki daya kacal a Turkiyya.

Ga sauran wasannin da za a buga:

Liverpool vs FC Basel Juventus vs Atl Madrid Olympiakos vs Malmö FF Real Madrid vs Ludo Razgd Benfica vs Bayer Levkn Monaco vs Zenit St P Bor Dortmd vs Anderlecht