City ta kai wasan gaba a gasar zakarun Turai

Manchester City Roma Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City tana matsayi na biyu a teburin Premier

Kungiyar Manchester City ta kai wasan zagayen gaba a gasar cin kofin zakarun Turai karo na biyu a jere kenan, bayan da ta doke Roma da ci 2-0 a Italiya.

Nasri ne ya fara zura kwallon a minti na 60, kafin Zabaleta ya kara kwallo ta biyu saura minti hudu a tashi daga wasan.

Daya sakamakon wasan da suke rukuni daya Bayern Munich ce ta doke CSKA Moscow da ci 3-0

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

Bayern Mun 3 - 0 CSKA Roma 0 - 2 Man City Ajax 4 - 0 Apoel Nic Barcelona 3 - 1 Paris St G Chelsea 3 - 1 Sporting NK Maribor 0 - 1 Schalke Ath Bilbao 2 - 0 BATE Bor FC Porto 1 - 1 Shakt Donsk