Ancelotti ya yaba wa 'yan wasan Madrid

Real Madrid Ludogorets Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Madrid tana matsayi na daya a gasar La Ligar Spaniya

Carlo Ancelotti ya yaba wa 'yan wasan Real Madrid da suka kafa tarihin lashe wasanni 19 a dukkan karawa da suka yi, bayan da suka doke Ludogorets Razgrad da ci 4-0 a gasar cin kofin zakarun Turai.

Madrid ta kammala wasanninta a cikin rukunin gasar ba tare da an doke taba, kuma ta kafa tarihin yin hakan karo na biyu kenan da babu kungiyar da ta taba yin hakan.

Ancelotti ya ce ya san yana da kwararrun 'yan wasa kuma fitattu, duk da haka sun kafa wannan tarihin ne da saka kwazo da kuma nuna kware wa da jajurce wa.

Tarihin tsawaita lashe wasanni 19 da Madrid ta kafa ya sa ta karya wanda Barcelona ta kafa a kakar wasan 2005-06, inda ta lashe wasanni 18 a jere karkashin koci Frank Rijkaard.

Madrid mai rike da kofin zakarun Turai, saura wasanni shida ta goge tarihin da kulob din Brazil Coritiba FC ya kafa a shekarar 2011, inda ya lashe wasanni 24 a jere.