An rage wa Parma ta Italiya yawan maki

Parma Serie A Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Parma tana mataki na karshe a teburin Serie A

Hukumar kwallon kafar Italiya ta rage wa kulob din Parma na Italiya maki, sakamakon kasa biyan 'yan wasa albashinsu tun daga Nuwambar bara.

Hukumar ta rage wa kulob din maki, sannan ta kuma ci tarar shugaban Parma, Tommaso Ghirardi da daraktan kulob din Pietro Leonardi kudi Yuro 5,000.

Parma tana matsayi na karshe a teburin Serie A da maki biyar, bayan buga wasanni 14 a gasar bana.

Kulob din wanda ya kare a mataki na shida a bara, bai samu shiga gasar Europa League ba, bayan da ya kasa cika ka'idar yi wa 'yan wasansa rijista.