Aikin gina Filayen wasa a Equitorial Guinea

Teodoro Obiang
Image caption Karo na biyu kenan da Equitorial Guinea za ta karbi bakuncin gasar

Masu gina filin wasa na Mongomo na yin aiki tukuru don kammala daya daga cikin filayen wasanni hudu da za su karbi bakuncin gasar cin kofin Afirka a badi.

Mongomo shi ne garin da aka haifi shugaban kasar Equitorial Guinea Teodoro Obiang, kuma za su karfi bakuncin gasar ne tare da Ebebeyin da Bata da kuma Malabo.

Equitorial Guinea ta amince da karbar bakuncin gasar ne a watan jiya, bayan da hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta yi mata tayin hakan.

CAF ta janye bai wa Morocco daukar bakuncin gasar bayan kasar ta nemi hukumar ta dage wasannin sakamakon tsoron kamuwa da cutar Ebola.

Equitorial Guinea ta yi amfani da filayen wasa na Malabo da Bata lokacin da ta karbi bakuncin gasar kofin Afirka na 2012, lokacin da ta yi hadaka da Gabon.