Golan Leicester Schmeichel zai yi jinya

Kasper Schmeichel Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester ce ke matasyi na karshe a teburin Premier

Mai tsaron ragar Leicester City, Kasper Schmeichel, likitoci za su yi masa aiki, sakamakon karyewa da ya yi, kuma zai yi jinyar wata guda.

Golan dan kasar Denmark, mai shekaru 28, ya ji raunin ne a lokacin da suke atisaye ranar Alhamis, za kuma a yi masa aiki ne ranar Juma'a.

Leicester za ta kara da Manchester City a gasar Premier wasan mako na 16 ranar Asabar, kuma tuni kungiyar ta ce Ben Hamer ne zai kama mata gola.

Schmeichel, wanda ya koma Leicester daga kulob din Leeds a shekarar 2011, ya tsawaita kwantiraginsa da Foxes zuwa shekaru hudu.