UEFA ta ci tarar kulob din Tottenham

Tottenham FC Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tottenham ta nemi afuwar laifin da 'yan kallonta suka aikata

Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta ci tarar Tottenham kudi fam 11, 870, sakamakon samun 'yan kallonta da shiga filin wasa sau biyu a karawa da Partizan Belgrade a watan jiya.

Sau uku ana samun tsaiko lokacin da ake wasan a filin White Hart Lane, inda aka dinga bata lokaci da ya kai tsawon minti goma.

An nuna wani faifen bidiyo wanda ya nuna wasu mutane uku da suka haddasa shiga filin wasan da aka yi karo biyu.

Tottenham ta nemi afuwar abin da ya faru, kuma ta ce ba za ta sake sakaci hakan ya sake faruwa ba, kuma tuni ma ta tsare mutanen uku bayan kammala wasan.