Wenger ya gode wa magoya bayan Arsenal

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana matsayi na shida a teburin Premier

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya gode wa Magoya bayan kulob din yadda suka dinga rera wakar yabonsa a karawar da suka doke Newcastle a gasar Premier ranar Asabar.

Magoya bayan kulob din sun yiwa Wenger, mai shekaru 65, dan kasar Faransa ihu a tashar jirgin kasa, bayan da suka tashi wasan da Stoke City ta doke su 3-2.

Arsenal ta doke Newcastle da ci 4-1 a filinta na Emirates, kuma magoya bayan kulob din sun yi ta rera waka da cewar "Babu wani kamar Arsene Wenger".

Wenger ya ce daya daga cikin aikin mai horas wa shi ne ya lashe wasa, kuma idan ba su samu yin hakan ba suna jin bakinciki da takaici.

Arsenal tana matsayi na shida da maki 26 a teburin Premier,inda Chelsea wadda take mataki na daya ta bata tazarar maki 13 tsakani.