Dzeko da Kompany za su yi jinya

Vincent Kompany Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City tana matsayi na biyu a teburin Premier

'Yan kwallon Manchester City Edin Dzeko da Vincent Kompany za suyi jinya, kuma ba za su dawo taka leda ba har sai sabuwar shekara.

Dzeko ya ji rauni ne a kafarsa lokacin da yake motsa jiki kafin fara wasan da suka doke Leicester, shi kuwa kyaftin Kompany ya ji rauni ne lokacin da yake karawar.

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya ce bayan da aka tashi wasan da suka doke Leicester 1-0, sai a sabuwar shekara za su dawo taka leda.

Manchester City za ta karbi bakuncin Crystal Palace da Burnley kafin su ziyarci West Bromwich Albion a wasan karshe na cin kofin Premier a bana.