Marcos Rojo zai yi jinya

Marcos Rojo Hakkin mallakar hoto epa
Image caption United tana fama da yawan rauni da 'yan wasanta ke yin jinya a bana

Dan kwallon Manchester United mai tsaron baya, Marcos Rojo, ya shiga cikin jerin 'yan wasan kulob din masu yin jinya.

An canja dan wasan dan kasar Argentina, mai shekaru 24 da Phil Jones a karawar da za suyi da Liverpool, sakamakon raunin da ya ji a filin atisaye.

Sauran 'yan wasan United masu tsaron baya da suke yin jinya sun hada da Chris Smalling da Luke Shaw da kuma Rafael.

Haka ma sauran 'yan wasan da suke yin jinya sune Angel Di Maria da Daley Blind da kuma Jesse Lingard.