Tottenham ta doke Swansea 2-1 har gida

Swansea Tottenham Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham tana matsayi na bakwai a teburin Premier

Swansea ta sha kashi a hannun Tottenham da ci 2-1, a gasar Premier wasan mako na 16 da suka kara a filin wasa na Liberty ranar Lahadi.

Harry Kane ne ya fara zura wa Tottenham kwallo a raga, kafin Swansea ta farke kwallonta ta hannun Wilfried Bony.

Tottenham ta kara kwallo ta biyu a raga da ya ba ta damar hada maki uku ta hannun Christian Eriksen daf da a tashi wasan.

Tottenham ta koma mataki na bakwai a teburin Premier da maki 24, yayin da Swansea ke matsayi na na tara da maki 22.