'Yan kwallon Zambia uku na asibiti

Zambia Players Accident Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zambia tana cikin gasar cin kofin Afirka da za a fara a badi

An kai 'yan wasan tawagar kwallon kafar Zambiya su uku asibiti domin kulawar gaggawa, sakamakon hatsarin da ya rutsa da su.

'Yan wasan uku sun hada da Nyambe Mulenga na Zesco United da Changwe Kalale na Power Dynamos da kuma Satchmo Chakawa na kulob din Green Eagles.

Hatsarin ya rutsa da 'yan wasan ne lokacin da suke yin bulaguro zuwa Lusaka a cikin karamar motar kulob din Zesco United.

'Yan kwallon sun yi hatsarin ne a Kibwe kan hanyarsu ta isa sansanin tawagar kwallon kafar kasar da suke shirin buga gasar cin kofin Afirka na badi.

Zambia tana rukuni na biyu da ya kunshi kasashen Jamhuriyar Congo da Cape Verde da Zambia a gasar da za a fara daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun badi a Equitorial Guinea.