Algeria ta gayyaci Abeid cikin tawagarta

Mehdi Abeid Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Algeria ce ke matsayi na daya a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka

Kocin Algeria, Christian Gourcuff, ya gayyato dan wasan Newcastle, Mehdi Abeid, cikin tawagar 'yan wasan da za su wakilce ta a gasar cin kofin nahiyar Afirka na badi.

Wannan ne karon farko da dan wasan zai buga wa Algeria kwallo, kuma daya daga cikin 'yan wasa biyar da kasar ta canja daga cikin wadanda suka buga mata gasar kofin duniya da aka kammala.

Abeid, wanda ya wakilci kasar a wasan neman tikitin shiga gasar Olympic a shekarar 2011, kuma wasanni uku kacal ya buga wa Newcasle a gasar Premier bana.

Algeria tana rukuni na uku da ya kunshi Ghana da Senegal da kuma Afirka ta Kudu a gasar cin kofin Afirka da za a fara daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun badi.

Ga jerin 'yan wasan za su wakilci Algeria a gasar cin kofin Afirka:

Masu tsaron baya: Rais Mbolhi (Philadelphia Union, USA)), Doukha Izzeddine (JS Kabylie) Mohamed Lamine Zemmamouche (USM Alger).

Masu tsaron baya: Essaid Belkalem (Trabzonspor, Turkey), Madjid Bougherra (Fujaira, UAE), Faouzi Ghoualm (Napoli, Italy), Rafik Halliche (SC Qatar, Qatar), Aissa Mandi (Stade Reims, France), Carl Medjani (Trabzonspor, Turkey), Djamel Mesbah (Sampdoria, Italy), Mehdi Zeffane (Lyon, France)

Masu buga tsakiya: Nabil Bentaleb (Tottenham, England), Yacine Brahimi (Porto, Portugal), Medhi Lacen (Getafe, Spain), Saphir Taider (Sassuolo, Italy), Mehdi Abeid (Newcastle United, England), Foued Kadir (Real Betis, Spain)

Masu wasan gaba: Abdelmoumene Djabou (Club Africain, Tunisia), Sofiane Feghouli (Valencia, Spain), Riyad Mahrez (Leicester City, England), Islam Slimani (Sporting Lisbon, Portugal), Hilal Soudani (Dinamo Zagreb, Croatia), Ishak Belfodil (Parma, Italy)

Masu jiran karta kwana: Liassine Cadamuro (Osasuna, Spain), Adlene Guedioura Adlane (Watford, England), Mehdi Mostefa (Lorient, France), Walid Mesloub (Lorient, France), Ryad Boudebouz (SC Bastia, France), Ahmed Kashi (Metz, France), Baghdad Bounedjah (Etoile du Sahel, Tunisia)