Mignolet zai zama "dumama benci"

Simon Mignolet Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Liverpool tana matsayi na 10 a teburin Premier

Kocin Liverpool, Brendan Rodgers, ya ce ya canja mai tsaron ragar kulob din Simon Mignolet nan take, ya kuma maye gurbinsa da Brad Jones.

Jones, dan kasar Belgium, shi ne ya tsare ragar Liverpool a karawar da Manchester United ta doke su 3-0, kuma shi ne zai kama wasan Capital One da Bournemouth.

Rodgers ya ce ya yanke hukuncin canja Miglonet ne domin gyare-gyaren da yake yi, da nufin karfafa kulub din a gasar wasannin da take buga wa.

Kocin ya kuma ce ya gamsu da yadda Jones, mai shekaru 32, ya taka leda a karawar da suka yi da United a Old Trafford.

Haka kuma kocin na fatan Miglonet, mai shekaru 26, zai dawo tagomashin sa.