Ronaldo ne gwarzon BBC da yafi haskakawa a bana

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Madrid tana Morocco domin buga gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyoyi

Dan kwallon Real Madrid, dan kasar Portugal ya lashe kyautar BBC ta bana, a matsayin dan wasan waje da yafi haskakawa.

Ronaldo, mai shekaru 29, kuma tsohon dan kwallon Manchester United, kuma shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya watanni 11 da suka wuce.

Ronaldo wanda ya zura kwallaye 281 daga cikin wasanni 267 da ya buga wa Real Madrid kwallo, ya gode wa jami'an BBC da suka zabo shi, sannan suka karrama shi.

Ya kuma lashe kyautar ne, bayan da ya doke 'yar kwallon tennis Serena Williams da Floyd Mayweather mai wasan damben boxing da kuma mai tseren babur Marc Marquez.

Shi ne dan wasan kwallon kafa na biyu da ya lashe kyautar, bayan da dan wasan Brazil Ronaldo ya fara dauka a shekarar 2002.

Ga jerin 'yan wasan da suka lashe kyautar a baya:

2013: Sebastian Vettel (Germany, F1) 2012: Usain Bolt (Jamaica, athletics) 2011: Novak Djokovic (Serbia, tennis) 2010: Rafael Nadal (Spain, tennis) 2009: Usain Bolt (Jamaica, athletics) 2008: Usain Bolt (Jamaica, athletics) 2007: Roger Federer (Switzerland, tennis) 2006: Roger Federer (Switzerland, tennis)