Mulenga ba zai buga gasar kofin Afirka ba

Zambiyan Players Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zambia ta kadu da jin labarin hatsarin da 'yan wasanta suka yi

Dan kwallon Zambia, Nyambe Mulenga, ba zai buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a fara a watan Janairu, sakamakon karaya da ya yi a kafarsa.

Dan wasan mai tsaron baya, wanda ba zai buga gasar wasan kwallon kafa mafi girma a nahiyar Afirka da Equitorial Guinea za ta karbi bakunci, saboda jinyar makwanni 12 da zai yi,

Mulenga, dan kwallon Zesco United, yana daga cikin 'yan wasan Zambia da suka yi hadari a mota lokacin da suke kan hanyar halartar sansanin horan tawagar kwallon kafar kasa.

Sauran 'yan wasan da hatsarin ya rutsa da su a garin Kabwe, sun hada da Kalale na Power Dynamos da Chakawa na Green Eagles.

Za a fara gasar cin kofin Nahiyar Afirka ne tsakanin 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun badi.