Rodgers ya karyata rashin jituwa a Liverpool

Brenda Rodgers Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Liverpool tana fama da koma baya a gasar wasannin bana

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya karyata jita-jitar cewa akwai rashin jituwa da sabani tsakanin 'yan wasan kulob din.

Liverpool wadda aka cire ta daga gasar cin kofin zakarun bana, tana matsayi na 11 akan teburin Premier.

Rodgers ya ce ya sha jin wadannan jita-jitar cewar babu kwanciyar hankali a Liverpool, amma yana tabbatar da cewa kan 'yan wasan kulob din a hade yake.

Liverpool za ta kara da Bournemouth a League Cup wasan daf dana kusa da karshe ranar Laraba, sannan ta karbi bakuncin Arsenal a gasar Premier.