De Gea zai ci gaba da wasa a Old Trafford

David De Gea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Golan ya kwashe shekaru uku a Manchester United

Manchester United ta ce tana da tabbacin cewar mai tsaron ragarta David De Gea, zai ci gaba da buga tamaula a kulob din.

Dan wasan, dan kasar Spaniya mai shekaru 24, kwantiraginsa za ta kare da United a shekarar 2016, kuma Real Madrid na sha'awar sha.

United ba ta ce ta fara tattaunawa da golan ba domin tsawaita kwantiraginsu, koda yake sai saura watanni 18 yarjejeniyar da suka kulla a baya za ta kare, sannan ne za su gana.

De Gea ya taka rawar gani a wasan da suka doke Liverpool 3-1, kuma ya koma United ne daga Atletico Madrid a shekaru 2011.