'Yan sandan Spaniya na binciken kisan dan kallo

Spain fan Kill
Image caption An dade ana kiraye-kiraye kan tada yamutsi a wasan kwallon kafa

'Yan sandan kasar Spaniya sun tsare mutane 32 dangane da binciken da suke yi kan kisan da aka yi wa wani magoyin bayan kulob din kwallon kafa.

Tun a cikin watan Nuwamba ne 'yan sandan suka tsare mutane biyu da suke zargi da hannu a kisan magoyin bayan Deportivo La Coruna, Francisco Javier Romero Taboada a Madrid.

Sauran mutane 30 da aka tsare ana bincikensu da laifuffuka da suka haddasa yamutsi kafin a fara wasa tsakanin Atletico Madrid da Deportivo La Coruna.

Magoya bayan kungiyoyin biyu sun yi batakashi a Madrid, dalilin da ya sa aka jikkita mutane 11.

Dukkan kungiyoyin biyu sun yi Allah wadai da tashin hankalin da magoya bayan suka yi.