Wenger na tunanin aikin da zai bai wa Henry

Invincible Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal tana matsayi na shida a teburin Premier

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce Thierry Henry yana da wasu muhimman dabi'un da suka wajaba a duk wani koci ya mallaka.

Henry, mai shekaru 37, wanda ya yi ritaya daga buga kwallon kafa a cikin makonnan, ya shaida wa jaridar Daily Telegraph cewa zai so ya sami damar horar da kulob din Arsenal.

Arsene Wenger wanda shi ne ya dauko Henry zuwa Arsenal a shekarar 1999 ya ce nan gaba akwai ranar da Henry zai yi aiki da kulob din a matsayin koci ko darakta ko dai wani mukamin.

Henry wanda ya koma aikin jarida, yanzu haka yana zuwa makarantar koyon aikin horar da kwallon kafa.

Ga jerin kungiyoyin da Henry ya buga wa tamaula:

2010-2014: New York Red Bulls

2007-2010: Barcelona

1999-2007: Arsenal (da kuma wasan aro da ya yi a 2012)

1999-1999: Juventus

1994-1999: Monaco