FIFA za ta binciki dalilin ritayar Garcia

FIfa Investigator Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin wasu jami'an FIFA da cin hantsi kan karbar bakuncin gasar kofin duniya

Mai kula da da'ar ma'aikata na hukumar FIFA mai zaman kansa Michael Garcia ya ajiye aikinsa saboda rikon sakainar kashi da ya ce ana yi wa binciken da ya yi.

Garcia ya yi bincike ne kan yadda aka karbi bakuncin gasar cin kofin duniya na 2018 da kuma 2022 da aka yi a shekarar 2010.

Mai binciken dan Amurka ya ce ya ajiye aikin ne saboda rashin kyakkyawan shugabanci daga hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Garcia ya ce ba shi da kwarin gwiwa akan binciken da lauyan Jamus Joachim Eckert mai zaman kansa ya gudanar tare da kwamitin da'ar ma'aikata.

Rasha ta samu izinin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na 2018, yayin da Qatar ta samu tikitin karbar bakuncin wasannin 2022.

Hukumar FIFA ta wallafa takaitaccen rahoton da Garcia ya gudanar da bincike mai dauke da shafi 430 zuwa shafuka 42.