Kungiyoyin Turai na son a buga kofin duniya a Mayu

Sepp Balatter Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sepp Blatter yana fama da kalubale a hukumar FIFA

Manyan kungiyoyin kwallon kafar Turai, sun bukaci da a gudanar da gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci a 2022 tsakanin 5 ga watan Mayu zuwa 4 ga watan Yuni.

An bai wa Qatar izinin karbar bakuncin gasar ne a shekarar 2010, kuma manyan jami'an FIFA sun bukaci a gudanar da gasar a lokacin sanyi.

Sai dai kuma kungiyar kulob kulob na kwallon kafa na Turai (ECA) da kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa sun ce zai fi kyau a gudanar da gasar a lokacin bazara.

Ana sa ran hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA za ta fitar da matsaya kan lokacin da za a yi gasar cin kofin duniya a Qatar a cikin watan Maris 2015.

A watan jiya ne dai FIFA ta sanar da cewa watakila a fara gasar cin kofin duniyar tsakanin Janairu ko Fabrairu ko kuma daga Nuwamba zuwa Disambar 2022.