Duka ne ya kashe dan wasan Kamaru Ebosse

Albert Ebosse Hakkin mallakar hoto
Image caption Hukukuntan Algeria sun ce jifa ne ya kashe dan wasan

Wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewa duka aka lakadawa dan wasan kwallon kafar Kamaru Albert Ebosse a Algeria, shi ne ya yi sababin mutuwarsa, sabanin rahoton da aka ce jifansa aka yi a ka tun farko.

Dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa ya mutu ne a cikin watan Agusta, bayan da kulob dinsa ya yi rashin nasara a gasar Algeria.

Rahoton da mahukuntan Algeria suka sanar ya ce dan kwallon ya mutu ne sakamon jifansa da aka yi da wani dutse mai kaifi.

Sai dai wani bincike da iyalansa suka sa aka yi, ya gano cewa Ebosse yasha dukan kawo wuka ne; al'amarin da ake tsammani ya faru ne a lokacin da suka shiga dakin hutun 'yan wasa.