Jak Alnwick ne zai kama wasa da Sunderland

Jak Alnwick Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Newcastle na fama da 'yan wasa masu yin jinya

Matashin golan Newcastle, Jak Alnwick, ya murmure zai kuma iya buga karawar da za suyi da Sunderland a gasar Premier.

Mai tsaron ragar, mai shekaru 21, ya ji rauni ne a kafadarsa a karawr da Tottenham ta doke su 4-0 a gasar Capital One Cup wasan daf da na kusa da karshe ranar Laraba.

Tuni mai kamawa Newcastle wasanni Tim Krul da mataimakinsa Rob Elliot suke yin jinyar, kuma kulob din ya fito da Freddie Woodman mai shekaru 17 a matsayin kar ta kwana.

Woodman zai sake zaman benci a wasan hamayyar da za su kara da Sunderland a gasar Premier wasan mako na 17 ranar Lahadi.