Manyan abubuwa 5 da suka faru a wasanni a bana

Sporting Moment Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Suarez a lokacin da ya yi cizo a karo na uku kenan

Shekarar 2014 tana kunshe da abubuwan tarihi masu kayatarwa a gasar cin kofin duniya, wanda kuma za a dade ba a manta ba a fagen wasanni, Haka kuma shekarar tana dauke da abubuwa marasa dadi da wadanda suka jawo cece-kuce. Wakilin BBC Stephen Fottrell ya zakulo manyan batutuwan da suka fi jan hankali a shekarar, da kuma labaran da suka fi jan hankali a kafar sada zumunta.

Jamus ta kunyata Brazil a gasar cin kofin duniya

Kasar Jamus ce ta lashe kofin duniya da aka kammala a Brazil, kuma yadda aka yi bikin murnar tarbar tawagar 'yan wasan a Berlin ya kasance daya daga cikin bikin da aka fi bibiya a kafar sada zumunta a duniya. Sai dai kuma ba za a taba mantawa da yadda Jamus ta casa Brazil mai masaukin baki da ci 7-1 a wasan daf da na karshe. Yadda 'yan wasan Brazil suka dinga sharbar kuka a gaban 'yan kallonsu ya ja hanklin masu sha'awar kwallon kafa, ganin yadda aka yi wa Brazil karkashin jagorancin kwararren kocinta Luiz Felipe Scolari inda aka zura mata tarin kwallayen da ba a taba zura wa wata kasa ba a gasar cin kofin duniyar.

An dakatar da Suarez buga wasanni bayan da ya ciji Chiellini

Wani labarin da ya ja hankalin mutane shi ne na dan kwallon Uruguay Luis Suarez lokacin da ya ciji dan wasan Italiya Giorgio Chiellini a wasan da kasashensu suka kara a gasar cin kofin duniya. Tun kafin gasar kofin duniya an dakatar da Suarez sau biyu daga buga wasanni sakamakon samunsa da laifin cizo a lokutan wasa, saboda haka lokacin da dan wasan ya kara aikata laifin cizo a karo na uku ya bai wa mutane mamaki matuka. An hukunta Suarez ta hanayr hana shi buga wasan kwallon kafa da shiga harkar wasannin tsawon watanni hudu, kuma a lokacin ne ya bar kulob din Liverpool ya koma Barcelona ta Spaniya kan kudi sama da fam miliyan 75.

Mayar da martani kan mutuwar Phillip Hughes

Mabiya wasan kwallon kruket sun yi takaicin mutuwar dan wasan Australiya, Phillip Hughes, kuma mutuwar tasa ya sa masu sha'awar wasan kwallon ba za su manta da ita ba. Hughes mai shekaru 25 ya gamu da ajalinsa a lokacin da aka bugo kwallon kruket ta doki wuyansa a lokacin da suke karawa da kasar Afirka ta kudu a Sydney. Mutuwar dan wasan ta sa abokan wasansa da 'yan kallo kuka sharbe-sharbe da kuma masu bin wasan sau da kafa.

Stephanie Roche 'yar kwallon kafar Ireland ta ja hankalin jama'a a You Tube

Lokacin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar da sunayen 'yan wasan da za a zabi wanda ya fi cin kwallo a wannan shekarar, sai aka yi tsammani za a ga sunayen 'yan wasa da suka hada da Robin van Persie ko James Rodriguez, amma sabanin hakan sai ga sunan Stephanie Roche a cikin 'yan takara. 'Yar wasan 'yar kasar Ireland mai taka leda a kulob din Peamount United ta samu wannan matsayin ne bisa kwallon da ta zura mai ban sha'awa a raga, wanda sama da mutane miliyon uku ne suka kalli kwallon da ta zura a shafin intanet na You Tube. Haka kuma 'yar wasan ta samu kulub a Faransa, haka kuma tana cikin 'yan takarar da za a fitar, a kwallon da aka ci mai ban mamaki a shekarar nan. Kuma zabo ta da aka yi kasancewarta macen farko a takarar yasa ta samu dumbin mutane suna ta yi mata kamfe din lashe kyautar da za a fitar da wanda ya samu a ranar 12 ga watan Janairu a Zurich.

'Yar damben boxing din kasar Indiya Sarita Devi ta ki karbar lambar yabo

Cece-kucen da ya fi jan hankali a wasan damben boxing a shekarar nan bai wuce lokacin da 'yar wasan Indiya Sarita Devi ta ki karbar lambar yabo a lokacin da za a rataya mata lambar azurfa a gasar wasannin nahiyar Asiya ba. 'yar wasan ta ki karbar lambar yabon ne saboda a cewarta an yi mata rashin adalci a dambatawar da suka yi da 'yar wasan Koriya ta Arewa Park Ji-Na. Halin da ta nuna ya sa hukumar wasan damben boxing ta dakatar da ita, amma ta nemi afuwa bisa laifin da ta aika ta.